Addini da RayuwaLabaraiWasanni

KATSINA: Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa kan iyayen dalibai 600 da aka sace a makarantar kwana ta Kankara

KATSINA: Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa kan iyayen dalibai 600 da aka sace a makarantar kwana ta Kankara

Jami’an yan sanda sun rika harbawa iyayen daliban yara na Sakandaren kwana ta maza, GSSS Kankara a jihar Katsina kafin suka tarwatsa su bayan da sukayi dafifi a ciki da wajen makarantar suna duba ‘yayansu,

Wannan dai na zuwa ne bayan da rahoto ya bulla cewa yan bindiga sun kai hari makarantar a daren jiya Juma’a inda ake fargaban dalibai 600 sun bata.

Iyayen yara a harabar makarantar

Majiyoyi sun shaidawa Manuniya cewa Gwamnan jihar Katsina, Masari ya ziyarci makarantar inda iyaye suka rika yi masa iface-iface suna neman sai ya fito masu da ‘yayansu lamarin da ya jawo dakyar yan sanda suka kubutar dashi ta hanyar rika harba barkonon tsohuwa.

Kawo yanzu dai babu hakikanin adadin daliban da aka sace ko suka bata a harin a hukumance amma dai mahukunta sun ce sun kubutar da dalibai 200 cikin dalibai 800 maza dake karatu a makarantar.

Harin daliban dai yana zuwa ne kasa da awa 24 da shugaban kasa Manjo Janaral Muhammadu Buhari ya sauka a jihar Katsina domin yin hutun mako guda.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button