Addini da RayuwaAlbum/EPWasanni

(Hotuna) Hadarin mota ya kashe matasa 3 a Kaduna

Innalillahi wainna ilaihi rajiun kalli hadarin motar da ya lakume ran mutane 3 a daren jiya a jihar Kaduna

Daga Manuniya

Akalla kwana 1 kenan da daukar hoton da kuke gani na matasan tare da shugabansu wato Rabiu Biyora. Inda suka sanya a shafin kamfaninsu suna yiwa mutane fatan alkhairi ashe-ashe na bankwana ne.

Matasan tare da shugabansu jim kadan kafin su kama hanyar Kaduna

Manuniya ta ruwaito hadarin ya rutsa matasan, Usman Bala da Yusuf Yahaya Isa Gama da kuma Babangida Dahiru a bayan ginin majalisa dokoki ta jihar Kaduna

Matasan dai sun shiga jihar Kaduna ne domin gudanar da shirye-shirye na taron wata kungiyar marubutan Arewa, mai suna Arewa Writers Association wacce ke da taro a Kaduna ranar Lahadi 13 ga watan Disamba 2020. Kazalika matasan suna aiki ne tare da kamfanin wani matashi a Kano, Rabiu Biyora wato Fafutuka Nigeria Limited.

Motar da suke ciki
Bayan motar da suke ciki
Gawar matasan

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button