Labarai

DA DUMI-DUMI: Shugaban jaridar Leadership Sam Nda-Isaiah ya rasu

Manuniya ta samu labarin rasuwar mawallafin jaridar Leadership, kana tsohon dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC, Sam Nda-Isiah,

Margayin ya rasu yana da shekara 58.

Kodayake dai kawo wannan lokacin da muke wallafa labarin ba a sanar da musabbabin rasuwar tasa ba amma dai majiyar Manuniya jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito margayin ya rasu ne da misalin karfe 11 na daren ranar Juma’a.

An haifi Mista Nda-Isaiah a Minna ta jihar Niger a 1962, kafin rasuwarsa shine ke rike da mukamin Kakaki Nupe, kuma ya karanci harkar magani a jam’iar Obafemi Awolowo.

Ya kasance marubuci ne mai sharhi akan alamuran yau da kullum kafin ya kafa kamfanin Leadership Newspaper Group a 2001.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button