Hausa SongsHausa VideoLabarai

DA DUMI-DUMI: El-rufai ya sake killace kansa bayan wasu na jikinsa sun kamu da korona

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya sanar da sake killace kansa biyo bayan samun wasu makusantansa da suka kamu da cutar korona

Manuniya ta ruwaito Gwamnan ya fitar da jawabi cikin bidiyo ga al’ummar jihar Kaduna da su kula da kansu musamman a wannan lokaci na bukukuwan karshen shekara

Ya ce su  kula da wanke, da bayar da tazara da gujewa cinkoso da sanya takunkumin da sauran dokokin kare kai daga kamuwa ko yada annobar.

Mista Elrufai ya ce a gwajin da akayi na baya-bayan nan an samu manyan jami’an Gwamnatinsa ciki har da wasu na jikinsa ko iyalinsa dauke da cutar korona, saboda haka daga yau Asabar ya killace kansa har zuwa ranar Lahadi da za a je ayi masa gwajin cutar.

Gwamnan El-Rufai yayin da yake jawabi a sabon bidiyo da ya fitar a daren ranar Juma’a

Ya kuma sha alwashin bayyanawa al’ummar jihar halin da ake ciki. Amma kafin nan ya killace kansa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button