in , ,

Babban Alkalin jihar Kano ya saki fursunoni 37

Babban alkalin Kano, Justice Nura Sagir Umar ya saki fursunonj 37 daga gidan yarin jihar Kano a karkarshin shirin Gwamnatin tarayya na rage cinkoso a gidajen yari

Manuniya ta ruwaito an baiwa kowane daga cikin fursunonin da akayiwa afuwa Naira dubu Bibbiyu (#2000) a matsayin kudin motar komawa cikin iyalansa.

Sai dai an ja kunnensu tare da horonsu da su dauki darasi daga abunda ya samesu su kasance mutane na gari da kowa zai yi koyi dasu a cikin jama’a sannan su kaucewa fadawa ko aikata laifuka

Kanawa 16 sun mutu a hadari mota da ya rutsa dasu a hanyar Kaduna

Jakadan Nigeria a kasar Amurka ya rasu