in , ,

Kanawa 16 sun mutu a hadari mota da ya rutsa dasu a hanyar Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce mutane 16 yan jihar Kano da suka rasu a hanyar Kaduna zuwa Abuja tayarsu ce ta fashe sukayi hadari ba yan bindiga ne suka kai masu hari ba.

Manuniya ta ruwaito Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jiharsa Kaduna Samuel Aruwan yana cewa binciken da sukayi ya nuna matafiyan sun gamu da ajalinsu ne a daidai garin Rigachikun dake kan hanyar Kaduna zuwa Zaria bayan da tayar motarsu ta fashe.

Muna addu’ar Allah ya jikan matafiyan da sauran mamatanamu baki daya. Allah ya basu hakurin jure rashi

Za a kafa hukumar Hisbah a Sokoto domin dakile yaduwar barna a jihar

Babban Alkalin jihar Kano ya saki fursunoni 37