in , , ,

An kona wasu mata 2 kurmus bisa zarginsu da satar mutane a jihar Osun

Fusatattun matasa a yau Alhamis sun cinnawa wasu mata 2 wuta sun kone su kurmus bayan kama su da zargin satar yara a garin Ojude Oba dake Iwo, a jihar Osun.

Manuniya ta ruwaito mutanen su Uku ne biyu mata da wani namiji suka je satar yaran a yankin Ori Eru amma sai sukayi rashin sa’a aka gano su aka kama su. Sai dai nan take shi namijin ya samu ya tsere a yayinda aka kama matan su 2.

Rahotanni sun nuna nan take yan garin suka kwashi matan zuwa fadar sarkin garin wato fadar Oba a inda suka nakada masu dukan kawo wuka sannan suka cinna masu wuta suka kone su kurmus.

DA DUMI-DUMI: Maina ya yanke jiki ya fadi a kotu

Za a kafa hukumar Hisbah a Sokoto domin dakile yaduwar barna a jihar