Labarai

Pantami ya baiwa MTN,GLO,Airtel,9MOBILE umurni su dakatar da sayarwa ko yin rajistar sabbin layukan waya

Gwamnatin tarayya ta umurci duka kamfanonin sadarwa na waya dake fadin Nigeria su gaggauta dakatar da sayar da sabbin layukan waya ko yin ragistar su.

Manuniya ta ruwaito Ministan Sadarwa, Sheikh Ali Isah Pantami ya baiwa hukumar kula da kamfanonin sadarwa NCC da su tabbatar MTN, GLO, 9mobile, Airtel da duka sauran kamfanonin sadarwa sun bi umurnin.

Ana dai ganin wannan mataki baya rasa nasaba da tsawatar-war da majalisa ta yiwa Ministan sadarwar kan ya dauki mataki bisa yadda ake amfani da lauykan waya ana sace jama’a ana karbar kudaden fansa da sauran ayyukan ta’addanci a Nigeria

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button