Labarai

Buhari ya fasa bayyana a gaban majalisa

Majalisar dokoki ta tarayya ta janye gayyatar da tayi wa Shugaban kasa Janaral Muhammadu Buhari domin ya bayyana a gabanta ya amsa tambayoyi kan tabarbarewar tsaro da aka shirya zai yi a ranar Alhamis

Matakin janye gayyatar na zuwa ne bayan da majalisar ta fahimci shugaban kasar ba zai hallara gabanta ba kamar yadda aka bayyana tun farko.

Manuniya ta ruwaito dama dai a wata ganawa da Janar Buharin yayi da Gwamnonin Nigeria a daren ranar Talata an tafka zazzafan muhawara kan bayyanar Buharin a gaban majalisar inda wasu Gwamnonin ke ganin kada ya amsa goron gayyatar

Ance Gwamnonin sun yi fargaban cewa muddin Shugaban ya je gaben majalisar to su ma majalisun dokokin jihohinsu zasu raina su su rika gayyatarsu suma a jihohinsu wanda suke ganin yin hakan tamkar raini ne.

Rashin bayyanar shugaban kasar ya kara bayyana karara yadda shuwagabannin Nigeria basu damu da rayuka da dukiyoyin talakawan da suka zabe su ba.

Yanzu dai yan Nigeria sun zura ido su ga ko shugaban zai bayyana ko kuwa zai yi bris.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button