LabaraiWasanni

Ofishin Jakadancin Nigeria a Jamus ya kori jami’in dake zina da mata kafin ya basu fasfo

Ofishin jakadancin Nigeria a kasar Jamus ya kori wani babban jami’in hukumar mai suna Martins Adedeji Oni, bayan samun sa da laifin rika yin zina da mata kafin ya basu fasfo dinsu

A watan Nuwamba ne dai Manuniya ta fallasa Mista Martins bayan ta fitar da rahoton wani bidiyo da ta samu na jami’in inda yake lalata da matar aure duk da cewa ta cika duka ka’idojin samu fasfo amma ya ce ba zai bata ba har sai ta amince masa.

A ranar 17 ga watan Nuwamba ofishin jakadancin ya ce ya ga rahoton kuma zai yi bincike a inda a lokacin aka dakatar da shi har zuwa yanzu da aka tabbatar cewa zargin da ake yi masa gaskiya ne yana zina da mata sannan yana karbar cin hanci da almundahana a ofishin nasa

“A saboda haka hukumar fa godewa duka wadanda suka taimaka aka fallasa shi kuma za ta cigaba da daukar mataki kan duk wanda ya yi amfani da ofishinsa wajen aikata ba daidai ba”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button