Shugaban kasa Janaral Muhammadu Buhari yana ganawar sirri da duka Gwamnonin Nigeria 36 a fadarsa ta Aso Villa.
Ganawar dai bata wuce nasaba da yawaitar hare-haren ta’addanci da da tabarbarewar tsaro a mafi yawan jihohin kasarnan.
Kana kuma a ranar Alhamis mai zuwa ne ake sa ran Mista Buhari zai gurfana a gaban gamayyar sanatoci da yan majalisun kasar domin amsa tuhume-tuhume kan rashin tsaro a Nigeria
Ko a watan Nuwamba da ta gabata kididdiga ta nuna an kashe akalla mutum 216 a Nigeria kuma an yi garkuwa da mutum akalla 144 wanda mafi yawa an zubda jinin ne a yankin Arewacin Nigeria.