Labarai

APC ta rushe duka shugabannin ta daga matakin sama har zuwa mazabu

Jami’iyyar APC ta sanar da rushe duka shugabanninta daga matakin kasa har zuwa shiyyoyi zuwa jihohi zuwa unguwanni zuwa mazabu

Jam’iyyar ta kuma kori tsohon mataimakin shugaban Jam’iyyar APC na shiyyar Kudu maso Kudu Hilliard Eta saboda yaki janye karar da ya shigar da Jam’iyyar yana neman sai an ayyana shi a matsayin sabon shugaban Jam’iyyar na kasa.

Manuniya ta ruwaito a zaman Jam’iyyar na gaggawa da akayi yau Talata a fadar Shugaban kasa ta Aso villa ta rushe kwamitin Gwamna Mai Mala Buni a inda ta sake nada wani kwamitin mutum 13 a karkashin shugabancinsa domin ya cigaba da aikin da ya faru

Sabon kwamitin an bashi watanni 6 zai gama aikinsa zuwa ranar 30 ga watan Yuni 2021.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button