in ,

A watan Nuwamba kadai an kashe mutum 216 anyi garkuwa da mutum 144 a Nigeria –Rahoto

Kididdiga ta nuna a watan Nuwamba kadai an kashe akalla mutum 216 a Nigeria kuma an yi garkuwa da mutum akalla 144.

Manuniya ta ruwaito rahoton da cibiyar bincike ta Civic Media Lab. ta fitar ya nuna anfi kashe mutane a yankin jihohin Arewacin Nigeria inda aka kashe 180 daga cikin 216.

Kana kuma jihar Borno ta fi fuskantar mafi yawan kashe-kashen inda aka kashe akalla mutum 131.

Binciken ya nuna ana kuma samun yawaitar hare-haren kungiyoyin asiri a jihohin Edo da Delta inda aka kashe mutum 24.

Kashe-kashe da garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a Nigeria musamman a yankin Arewa

Mafi yawan Almajirai dake gararamba a tituna ba yan Nigeria bane –inji Ganduje

Ofishin Jakadancin Nigeria a Jamus ya kori jami’in dake zina da mata kafin ya basu fasfo