Labarai

Ko an sake bani shugabancin APC ba zan karba ba –inji Oshimole

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa da aka tsige Adams Oshiomhole ya sha alwashin cewa ba zai taba yarda ya amshi shugabancin jam’iyyar ba ko an sake maida masa.

Mista Oshimole ya ce baya fada da kowa kuma bai rike kowa a rai ba cikin wadanda suka shirya makirci suka yake shi har aka cireshi to amma kuma baya son mulkin jam’iyyar akai kasuwa.

Ya ce yana cike da alfahari da nasarorin da jam’iyyar APC ta samu a lokacin mulkinsa. A cewarsa tuni ya umurci lauyoyinsa su janye karar da ya shigar a kotu yana kalubalantar cireshi, domin ko da ma kotu ta sake maida masa mukamin ba zai karba ba, kuma koda jam’iyyar ta sake nemansa a kashin kanta domin ya dawo shugabancin jam’iyyar ta APC a cikin ruwan sanyi zai ce baya so.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button