Addini da RayuwaLabaraiWasanni

TURA TA KAI BANGO: Mutanen gari sun fatattaki yan bindiga har sun kashe mutum daya

Jama’ar gari sun yi kukan kura kan wasu yan bindiga da suka kai farmaki kauyen Duwaduwa dake jihar Bauchi inda suka kashe dan bindiga daya kana sauran suka tsere.

Manuniya ta ruwaito kakakin rundunar yan sandan jihar Bauchi, DSP Ahmed Mohammad Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin a sanarwar da ya fitar ranar Juma’a inda ya ce a daren ranar Talata ne abun ya faru.

Ya ce yan ta’addan sun raunata wani mutum Muhammadu Adamu kana suka gudu da sabuwar babur dinsa kirar Bajaj.

Sai dai yan garin sun kada yan ta’addan a guje inda har suka kama daya daga cikinsu mai suna Sani Alhaji Dalori suka kashe shi anan take.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button