in , ,

Ta leko ta koma: Jami’ar Amurka ta ce bata baiwa Ganduje Farfesa ba

Jami’ar East Carolina ta kasar Amurka, ECU, ta karyata sanarwar da Gwamnatin jihar Kano ta fitar cewa wai Jami’ar ta baiwa Gwamna Abdullahi Ganduje mukamin Farfesa.

Manuniya ta ruwaito a ranar Talata ne sakatare  yada labarai na jihar Kano, Abba Anwar, ya fitar da sanarwar cewa Jami’ar East Carolina ta kasar Amurka, ECU ta duba irin namijin ayyukan da Ganduje ke yi a Kano har ma ta aika masa da takardar nadashi Farfesa.

Daga nan ne ma aka fara sanya Farfesa a hade da sunan Gwamnan,
Sai dai Jami’ar ECU din ta fitar da sanarwar cewa bata san da wannan magana ba, kuma ita bata bawa Gwamna Ganduje Farfesa ba.

An daura auren Mahmud yau kalli hotunan auren

TURA TA KAI BANGO: Mutanen gari sun fatattaki yan bindiga har sun kashe mutum daya