Hausa SongsLabarai

Kotun daukaka kara ta amince da hukuncin kisa da aka yankewa Maryam Sanda

Kotun daukaka kara dake Abuja a yau Juma’a ta goyi bayan hukuncin kisa da kotun farko ta yankewa Maryam Sanda, bisa kashe mijinta Bilyaminu Bello, da ta yi a ranar 19 ga watan Nuwamba 2017.

Tun da farko dai wani alkalin kotu a wata babban kotu dake Maitama a Abuja ne, Justice Yusuf Halilu a ranar 27 ga watan Janairu, 2020, ya yankewa Maryam hukuncin kisa bayan gamsuwa da yace kotu tayi da hujjojin da aka gabatar a gabanta dake nuna lallai itace ta sossokawa mijinta wuka har ya mutu.

Sai dai Manuniya ta ruwa Maryam, mai yara 2 ta daukaka kara a ranar 19 ga watan Fabairu 2020, tana mai rokon kotun daukaka karar da tayi watsi da hukuncin da babban kotun Abuja ta yanke mata na kisa sannan ta wanke ta ta sallame ta daga duka laifin kisan.

Sai dai ta taka rashin sa’a domin kuwa a zaman shari’ar yau Juma’a kotun daukaka karar ta jaddada hukuncin da kotun farkon ta yanke akanta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button