Addini da RayuwaHausa Songs

Yaro ya mutu daga gwada rataye kansa kamar yadda ya ga anayi a fim

Muna fata iyaye zasu lura su hankalta, A ranar Litinin din nan ne al’ummar jihar Lagos suka shiga alhini sakamakon wani matashin yaro karami da ya kashe kansa ta hanyar rataya.

Manuniya ta ruwaito lamarin ya faru ne da safiyar ranar Litinin da ta gabata.

Rahotanni sun bayyana cewar yaron ya gwada rataye kansa ne a fanka da nufin ya tabbatar ko ana iya mutuwa dagaske idan mutum ya rataye kansa kamar yadda ya saba ji da gani a fina-finai ko a labarai.

Kelvin bayan ya rataye kansa

Sai dai aikuwa ya taka rashin sa’a domin kuwa yaron ya mutu bayan rataye kan nasa kuma babu kowa a kusa balle a ceceshi har ya mutu.

Kalli hotunan yaron wanda aka bayyana sunansa da Kelvin.

Margayi Kelvin
Muna fata iyaye zasu dauki darasi akai

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button