Labarai

Nan da shekara 20 ma ba lallai a iya magance ta’addanci a Nigeria ba -Buratai

Shugaban sojin Nigeria Laftanar Janar Tukur Buratai ya yi martani ga masu kiraye-kirayen shugaban kasa da ya sauke su saboda sun gaza akan sha’anin tsaro.

Majiyar MANUNIYA ta ruwaito Mista Buratai ya ce mutane basu fahimci menene zurfin ta’addanci da tada kayar baya ba, ya ce a yanzu sai dai kawai ayi fatan kada ta’addanci ya yadu amma ana iya kara kwashe wasu shekara 20 ana fama da ta’addanci a Nigeria.

Yan Nigeria dai sun shiga kiraye-kirayen cewa Buratai da duka hafsoshi  tsaro su sauka bayan samun bullar hare-haren ta’addanci a kasar, na baya-bayan nan shine batum kashe manoman shinkafa 43 a kauyen Zabarmari dake jihar Borno.

Kodayeke majalisar dinkin duniya ta ce mutum fiye da 100 aka kashe a harin amma shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau a wani bidiyo ya ce mutum fiye da 70 ne suka kashe yankan rago kuma sunyi hakan ne saboda manoma na kama yan Boko Haram suna mikawa sojoji.

Tuni dai majalisar dokoki ta tarayya ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta sauke hafsoshin tsaron Nigeria saboda sun gaza, sannan shi ma din ya bayyana a gan majalisar domin amsa tambayoyi kan tabarbarewar tsaro a kasar nan da ya kasa magancewa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button