Addini da RayuwaAlbum/EPLabaraiWasanni

Laifin da yasa Boko Haram sukayi wa manoma 43 yankan rago a Borno

Manoman shinkafa 43 kenan da akayiwa yankan rago a safiyar jiya Asabar a Maiduguri!

Laifinsu shine su ba ‘yayan Buhari bane,
Laifinsu shine basu da alaka da Buratai
Laifinsu shine basu fito a dangin Sadiq ba,

Laifinsu shine basu da alaka da Gwamna Zulum,

Bayin Allah laifinsu shine basu zabi tada kayar baya ba,

Laifinsu shine shugaban kasa yace a fita ayi noma, sun amsa kira sun fita domin biyayya ga umurnin shugaban kasa…

Laifinsu basu zabi zama yan bindiga ko masu garkuwa da mutane suna karbar fansa ba!

Laifinsu shine sun fita neman abinci da zasu taimaki iyalansu su rufawa kansu da iyalansu da kasarsu asiri!

Laifinsu shine sun dauki amanar dukiyoyin su da rayukan su, cikin ruwa da sanyi da iska sun zabi GWAMNATIN da ta gaza rike amanar da ta dauka!

Yayin janaizar manoma 43 da Boko Haram suka yiwa yankan rago a Maiduguri

Kuma yanzu haka iyalansu suna ji suna ganin Gwamnati zata yiwa wadanda sukayi masu wannan ta’addacin afuwa, ta yi masu gata sannan ta sako su cikin al’umma su cigaba da hole rayuwarsu, shikenan sun kashe banza!!

Allah ya gafarta masu

Allah ya sakawa duk wanda aka zubar da jininsa, Allah ya bi masa hakkinsa, Allah ya saka masu…

Manoma 43 da aka yiwa kisan gilla

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button