Addini da RayuwaAlbum/EP

ZABE: Mata ne mataimakan duka yan takarar kananan hukumomi a jihar Kogi

Siyasa a jihar Kogi ta dauki sabon salo a inda binciken da Manuniya tayi ta fahimci cewa kusan duka mataimakan masu neman shugabancin karamar hukuma a karkashin jam’iyyar APC a jihar Mata ne.

Hon. Adejoh Friday ya zabi Hon. Blessing Aishat a karagar hukumar Olamaboro

Bayanai sun nuna hakan ya samo asali ne daga Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello inda ya sanya babbar mai kula dashi a fannin tsaro ADC dinsa yasa mace.

Daga nan kuma ya bukaci mata a jihar su tashi tsaye sosai su shiga a dama dasu a siyasa. Ana dai ganin wannan umurni ne tasa APC a jihar ta yanke baiwa mata mukaman mataimaki a zaben kananan hukumomin jihar dake tafe.

Shima Hon. Onoja James ya zabi Hon. Musa Ayisat a karamar hukumar Igalamela Odolu
Eng. Abdulrazak Muhammed ya zabi Misis Bilkisu A. Aliyu a karamar hukumar Okene
Hon. Joseph Omuya Salami ya zabi Hon. Mariam O. Hamzat a karamar hukumar Adavi

Dama dai tuni Gwamnan jihar ta Kogi Yahaya Bello ya zabi mace a matsayin babbar dogarinsa, wato ADC, inda ya nada ASP Ifeoma Akaya.

Babbar dogarin Gwamna Yahaya Bello, ASP Ifeoma Akaya a bakin aikinta.

Sai dai a yanzu jama’a sun zura ido su ga irin tasirin da sanya mata a matsayin mataimaka ko zai haifarwa yan takarar da mai ido. Sannan ana jiran aga ko yan takarar sauran jam’iyyun zasuyi wannan gamin gambiza.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button