Labarai

Yan bindiga sun sace iyalan dan sandan dake kula da lafiyar Atiku Abubakar

Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun haura gidan daya daga cikin jami’an yan sanda dake kula da lafiyar tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar sun sace matarsa da dansa.

Bayanai sun nuna lamarin ya faru ne a daren ranar Litinin a garin Yolde- Pate, dake Yola a jihar Adamawa. Ance yan bindigar sunyi kai harin ne da nufin sace dan sandan bayan sun samu labarin ya dawo daga tafiya tare da Atiku.

Sai dai majiyar Manuniya “the nation” ta ruwaito cewa yan bindigar sun taka rashin sa’a inda suka tarar dan sandan baya gida sai dai iyalansa.

Ana dai zargin yan bindigar suna zargin dan sandan na daya daga cikin na hannun daman tsohon shugaban kasar, watakila hakan ne ya tunzurasu suka tafi da matarsa da dansa da suka tarar a gida a lokacin.

A wani labari makamancin wannan kuma rahotanni sun nuna yan bindiga a jihar Adamawar sun sace wan shugaban masu rinjaye na majalisar jihar Adamawa Hamman Tukur Yetisuri.

Bayanai sun nuna yan bindigar sun je har gidan mutum ne dake garin Jada Mbulo da wajajen karfe 2 na dare inda suka rika harbe-harbe da bindiga har suka samu nasarar daukarsa ta karfi sannan suka tafi dashi tare da bukatar kudin fansa Naira miliyan N50.

Manuniya ta ruwaito kakakin rundunar yan sandan jihar Adamawa, DSP Suleiman Nguroje, ya tabbatar da faruwar lamarin guda biyu a inda yace suna bakin kokarinsu domin kubutar da wadanda akayi garkuwa dasu din sannan su hukunta masu garkuwar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button