in , ,

Wata ta jefar da jaririnta a bola kwana daya da haihuwarsa

Jama’a sun yi ta tofin Allah wadai game da rashin tausayi da wata mata ya nuna bayan da ta haifi jariri sannan kwana guda da haihuwar ta dauke shi ta jefar a bola.

Manuniya ta ruwaito lamarin ya faru ne a titin Ikwerre dake Mile 2 diobu a garin Portharcourt babban birnin jihar Rivers.

Jaririn da aka tsinta a bola

An tsinci jaririn ne da wajajen misalin karfe 9:30 na daren jiya Laraba. Sai dai ko da aka kai shi asibiti an tarar ya mutu.

Lokacinda aka tsinci jaririn
Sai dai ko da aka je asibiti ya riga ya mutu
Kungiyar kare yancin yara tayi Allah wadai da faruwar lamarin

An kama miji da mata dauke da tarin makamai a Katsina

MALAM YA FASA KWAI: Duk kashe-kashen da akeyi akwai hannun manyan kasarnan yan Arewa a ciki