LabaraiWasanni

Rashin tsaro: Majalisar dattijai ta nemi Pantami ya gurfana a gabanta don amsa tambayoyi

Majalisar dattawa a ranar Laraba ta bukaci Ministan Sadarwa, Dr. Isah Ali Pantami ya gurfana a gabanta domin ya yi mata bayani yadda ma’aikatarsa ta gaza dakatar da yan ta’adda daga yin amfani da waya wajen karban kudaden fansa idan sunyi garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta’addanci da ake yi ta hanyar amfani da waya ko hanyoyin sadarwa.

Manuniya ta ruwaito Sanata Emmanuel Bwacha mai wakiltar Taraba ta Kudu ne ya gabatar da kudurin a gaban majalisar inda ya ce matsalar tsaro a kasarnan kullum kara muni abun yake yi.

A cewar Sanata Bwacha a Nigeria ne kadai har yanzu yan ta’adda ke amfani da hanyoyin sadarwa wajen aiwatar da ta’addancinsu kuma su kwana lafiya saboda babu wata hanya ta zamani da za ayi amfani da fasaha wajen kama su.

Yace sha’anin garkuwa da mutane, fashi da makami da satar dabbobi da kisan kai da sauran miyagun ayyukan ta’addanci duk suna ta kara ta’azzara ne  a kasarnan saboda fannin sadarwar kasarnan bata aikin da ya kamata.

Sannan kuma ga wasu bata garin yan siyasa na amfani da matasa wajen kokarin tada zaune tsaye a Nigeria wanda duk shima wannan ya faru ne saboda rashin nagartar sashin sadarwa da kuma gazawar fannin tsaro.

Tuni dai Sanatoci suka goyi bayan kudurin da sanatan ya gabatar na neman Shehin malamin ya gurfana a Majalisar domin amsa tambayoyi akai.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button