Album/EPLabarai

An kama miji da mata dauke da tarin makamai a Katsina

Rundunar tsaron farin kaya ta SSS a jihar Katsina ta samu nasarar kama wasu ma’aurata Usman Shehu da matarsa Aisha Abubakar da jibgin harsasan bindiga nau’i daban-daban suna safararsu a sassan jihar.

Manuniya ta ruwaito an kama ma’auratan ne a ranar Lahadi da ta gabata a karamar hukumar Rimi.

Shugaban gamayyar tsaro, John Enenche, a yau Alhamis ya shaidawa manema labarai cewa an kama su ne a kauyen Abukur lokacinda suke hanyar rabar da makaman.

Ya ce daga cikin abunda aka kamasu dashi akwai magazin 14 na Bindigogi, da harsasai masu girman 9.6mm guda 61 da harsasai masu girman 7.62mm guda 399

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button