Album/EPHausa SongsLabarai

An kama magidanci da matarsa da dansa suna sana’ar sayar da wiwi a Kano

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wani matashi dan shekara 21 da sinki-sinkin tabar wiwi guda a Unguwar kofar Gadon Kaya.

Kakakin rundunar yan sandan Kano Haruna Kiyawa ya tattauna da matashin inda ya bayyana cewa “mahaifinsa ne ke sana’ar sayar da wiwin kuma fiye da shekara 20 kenan yana sayarwa”

Kabir da tarin wiwin da aka kamashi dasu

Manuniya ta ruwaito matashin mai suna Kabir Mahmud ya ce mahaifiyarsa ce ta kira shi a waya tace ta samu labari an kama mahaifinsa da wiwi saboda haka ya gaggauta ya zo gida ya kwashe ragowar wiwin da suka rage a cikin gidan don gudun kada jami’an tsaro su zo bincike laifi ya karu.

Sai dai Kabiru ya yi rashin sa’a domin bayan ya zo gida ya kwashi wiwin zai kai Unguwar Danbare gidan abokinsa ya boye sai yan sanda suka kama shi a hanya.

Kabir da abokinsa

Yanzu haka yan sanda sun kama mahaifiyar matashin, da abokinsa sannan suna cigaba da bincike domin gurfanar dasu a kotu

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button