Album/EP

An samu bullar wata sabuwar cuta mai hana fitsari a jihar Kogi, ta kashe mutum 50

RAHOTO: Wata cuta mai hana yin fitsari da kashi ta bulla a jihar Kogi, har ta kashe mutum 50

Majalisar dokokin jihar Kogi ta shelanta bullar wata cuta a jihar Kogi wacce ta kashe fiye da mutum 50 yan kasa da shekara 40 a karamar hukumar Olamaboro,

Alamomin cutar sun hada da sanya ciwon kai, sanya idanu suyi jajaye, rashin cin abinci, rashin yin fitsari ko bayan gida da kuma sanya rawar jiki.

Manuniya ta ruwaito har zuwa yanzu ba’a gane musabbabin cutar ba kuma abun tsoro game da ita shine yadda take kashe wanda ya kamu da ita a cikin mako guda.

Wani dadin abun tsoro game da cutar kamar yadda yan majalisar suka fadi shine bata jin magani daga na gargajiya har na bature

A saboda haka suka nemi ma’aikatar kiwon lafiya ta Nigeria da ta yi gaggawar bincike akai domin dakile yaduwar ta

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button